1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude bututun Nord Stream 1

Binta Aliyu Zurmi
July 21, 2022

Rasha ta bude bututun iskar gas na Nord Stream 1 da ke samar da makamashin gas ga kasashen Turai ta Jamus, bayan kammala aikin gyaran bututun.

https://p.dw.com/p/4ERSi
Deutschland | Nord Stream 1 in Lubmin
Hoto: Sean Gallup/Getty Images

 Da safiyar wanna rana ce aka bude bututun, sai dai babu tabbas game da adadin da za a  ci gaba da yin jigila ta wannan bututu mai mahimmanci don guje wa rikicin makamashi a cikin hunturu.

Tun farko Rashar ta dakatar da isar gas din ne saboda gyaran injinn bututun. Jamus da ke dogaro da kusan kaso 60 zuwa 70 na cikin dari na makamashin iskar gas din kasar Rasha na zargin mahukuntan Kremlin da amfani da makamashin a matsayin makamin yaki.

Kamfanin iskar gas mallakar kasar Rasha na Gazprom ya rage kaso 40 cikin dari na makamashin da ya ke turowa Jamus a makwannin baya.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya sha alwashin kamfanin zai ci gaba da tsayawa a kan sharudan da suka cimma tun da farko na sayar da makamashin ga kasashen Turai, duk kuwa da takaddamar da ke tsakaninsu.