1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na adawa da matakin soji a Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
August 11, 2023

Rasha ta jaddada adawarta ga duk wani mataki na amfani da karfi a Nijar, wanda a cewarta zai haifar da rashin zaman lafiya a kasar da yankin Sahel baki daya.

https://p.dw.com/p/4V5BE
Shugaban kasar Rasha Putin na adawa da amfani da karfin soji a jamhuriyar NijarHoto: Sergei Bobylyov/TASS/REUTERS

Rasha ta sake nuna adawa ga duk wani mataki na kutsawa Jamhuriyar Nijar da makamai don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerar mulki, inda ta ce amfani da karfi zai haifar da damuwa a wannan kasa ta yankin Sahel. A cikin wata sanarwar da ta fitar a birnin Moscow, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta yi imanin cewar matakin soji ba zai magance rikicin Nijar ba, sabanin haka ma zai iya haifar da rashin zaman lafiya tare da dagula al'amuran tsaro a yankin Sahel baki daya.

Sai dai gargadin na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin rundunonin sojojin kasashen yammacin Afirka ke shirin ganawa a birnin Accra na Ghana a ranar Asabar domin tsayar da dabarar yakar sojojin Nijar, kwanaki biyu bayan da shugabanni ECOWAS/CEDEAO suka ba da damar yin amfani da karfi wajen maida kasar da turbar dimokuradiyya.

Amma dai dubban magoya bayan gwamnatin mulkin sojan Nijar sun sake gudanar da zanga-zangar lumana a kusa da sansanin sojin Faransa da ke birnin Yamai domin nuna kyama ga kasar da ta yi musu mukkin mallaka.