Rikicin Kenya da Somaliya ya ɗauki sabon salo
October 31, 2011Ƙungiyar likitocin bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa wadda aka fi sani da suna Doctors Without Borders ta sanar da cewar fararen hula ukku ne suka mutu a yayyin da aƙalla wasu 50 kuma suka sami rauni sa'ilin da jirgin saman yaƙin ƙasar Kenya ya ƙaddamar da samame akan wani sansanin 'yan gudun hijirar dake cike da Mata da ƙananan yara a kudancin ƙasar Somaliya.
Sai dai kuma a martanin da ta mayar, rundunar sojin ƙasar ta Kenya ta yi watsi da zargin kissar fararen hular, kana ta ce ta ƙaddamar da hari ne tare da kissar wasu mambobin ƙungiyar mayaƙan Al-Shebab su 10.
Idan za'a iya tunawa dai tun kimanin makonni biyu kenan da gwamnain ƙasar Kenya ta tura dakarun ta zuwa sassa daban daban na kan iyakar ta da ƙasar Somaliya, a wani matakin da tace ke da nufin dakatar da ayyukan mayaƙan ƙungiyar Al-Shebab, wadda ake dangantawa da ƙungiyar Al Qaeda.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas