Rikicin Somaliya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa
October 7, 2011Za mu fara ne da sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta mai taken yaƙin da babu mai nasara a birnin Mogadishu. Ta ce dukkan mazauna Mogadishu sun yi jiran wannan lokaci tana mai nuni da mummunan harin da al-Shabaab ta kai babban birnin na Somaliya.
"Sanin kowa ne al-Shabaab ba za ta bar wannan birni ba tare da yaƙi ba. Duk cewa ƙungiyar ta yi rauni a yaƙin da take a Mogadishu da gwamnati riƙon ƙwarya da dakarun Afirka, amma hakan ba ya nufin an karya alƙadarin sojojin sa kan. A matsayin ta na ƙungiyar 'yan ta'adda tana da ƙarfi fiye da a lokutan baya kamar yadda harin na birnin Mogadishu ya nunar. Yayin da gwamnatin wucin gadi da masu tallafa mata daga ƙetare ke iya ƙoƙarin cin al-Shabaab da yaƙi, ita kuwa ƙungiyar tana samun kuɗin sayen makamai daga harkokin da ta ke yi a tashar ruwan Kismayu. Saboda haka jaridar ta ce ba wanda zai yi nasara a wannan yaƙi a yankin ƙahon Afirka."
Matsalar cututtuka da suka addabi yara a Somaliya
Ƙyanda ta zama wata mummunar cutar dake kashe yara a Somaliya, inji jaridar Kölner Stadt Anzeiger tana mai nuni da yadda cutar ta zama ruwan dare a tsakanin ƙananan yara a Somaliya. Jaridar ta rawaito wata ma'aikaciyar jiyya daga birnin Kolon da ba ta jimma da dawowa daga Mogadishu ba tana mai cewa a wani asibitin birnin Mogadishu da ta yi aiki na tsawon makonni uku, yawan yara da suka mutu ya fi wanda ta gani a tsawon rayuwarta. Ɗaukacinsu sun gamu da ajalinsu ne sakamakon kamuwa da cutar ƙyanda.
Neman ikon ma'adanan ƙarƙashin ƙasa a Najeria
Gwagwarmaya kan ma'adanan ƙarƙashin ƙasa a Najeriya, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali kan yadda Najeriya ke neman masu zuba jari na ƙetare domin sabunta ma'aikatun ƙasar. Ta ce yayin da China ke hanzari su kuwa Jamusawa ɗari-ɗari suke yi.
"Najeriya ƙasa ce mai arzikin ƙarƙashin ƙasa musamman ma man fetir da kuma iskar gas. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da ƙasashen duniya ke rige-rigen samun shiga ƙasar domin tabbatar wa kansu cin gajiyar ma'adanan ƙarƙashin ƙasa. Nahiyar Turai dai na asarar ɓangarorin zuba jari masu yawa a tarayyar ta Najeriya ga kamfanonin China."
Hana ba da kyautar UNESCO da sunan ɗan kama karya
Tarayyar Turai da ƙasar Amirka sun hana ba da kyautar ƙungiyar ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO da sunan shugaban mulkin kama karyar ƙasar Equitorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, inji Jaridar Die Presse tana mai rawaito kafofin diplomasiyya a birnin Brussels. Shugaban wanda yake kan mulki tun shekaru 32 da suka wuce bayan wani juyin mulki, ya kwashe watanni uku yana kai gwauro da mari domin a amince ya ɗauki nauyin wannan kyautar ta dala miliyan uku, inda ya yi nasarar shawo kan ƙasashen Afirka 13 waɗanda ke cikin majalisar gudanawar UNESCO domin mara masa baya. To sai dai dangane da mulkin kama karya da cin zarafin 'yan ƙasarsa da wasashe dukiyar ƙasar da iyalansa ke yi ya sa manyan ƙasashen duniya sun yi fatali da wannan yunƙuri na sa.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi