Rikicin ƙasar Somaliya da na fashin jiragen ruwa
May 30, 2009A rahotonta mai taken sabuwar Iraqi a yankin ƙahon Afirka jaridar Tageszeitung ta yi nuni da rikicin da ya rincaɓe a Somaliya dake kawo ciƙas ga yaƙin da ake yi da ´yan fashin jirgin ruwa da ´yan ta´adda. Ta ce jim kaɗan gabanin gwamnatin Jamus ta amince da faɗaɗa aikin dakarunta dake fatattakan ´yan fashin jirgin ruwa a gaɓar tekun ƙahon Afirka gwamnatin Somaliya ta yi ƙorafi ga ƙungiyoyin agaji na duniya tana mai barazana da jan kunnensu idan suka jibge kayan agaji a Mogadishu maimakon a raba su ga mabuƙata. Ta ce gwamnati da ta yi wannan barazanar yanzu tana iko ne da kashi ɗaya cikin uku na babban birnin sakamakonƙazamin faɗan da suke gwabzawa da sojojin sa kan Islama abin da ya tilastawa ƙungiyar agaji ta likitoci rufe wani asibiti kana kuma aka wawashe wata harabar asusun UNICEF.
Kamfanin haƙan mai na Shell a gaban kotu, taken rahoton da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta kenan game da shari´ar da ake ta hukuncin kisan da aka zartas kan Ken Saro-Wiwa a Najeriya. Ta ce shekaru 14 bayan aiwatar da hukuncin kisa kan marubucin na Najeriya yanzu kamfanin Shell na kare kansa a gaban wata kotu ta birnin New York bayan da ɗan Saro-Wiwa ya kai ƙarar kamfanin yana mai zarginsa da hannu a mutuwar mahaifin na sa. To sai dai kamfanin ya musanta wannan zargi. Jaridar ta ce marigayi Saro-Wiwa wanda ya sha gwagwarmaya ƙwatowa al´umar Ogoni haƙƙinsu musamman daga rashin adalci da gurɓata yanayin su da kamfanin shell ke yi, ya janyo masa baƙin jini a tsakanin hukumomin Najeriya a lokutan baya. Yanzu haka an ɗage zaman kotun zuwa mako mai zuwa. A wani labarin kuma jaridar ta rawaito ƙungiyar Amnesty International tana zargin dakarun tsaron gwamnatin da cin zarafin firsinoni da sauran waɗanda ke tsare a gidajen waƙafi.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi ga ƙoƙarin gwamnatin Belgium na tilastawa gwamnatin Senegal ɗaukar matakin hana tsohon shugaban Chadi dake gudun hijira a ƙasar, Hissene Habre tserewa. Kotun ƙasa da ƙasa ta birnin The Hague ta yi watsi da wannan buƙata ta Belgium bisa dalilan cewa tuni gwamnatin Senegal ta ba da tabbacin cewa ba zata yarda Habre ya bar ƙasar zuwa wata ba.
Ƙasashen Afirka Kudu da Sahara na da ta su damuwar maimakon su duƙufa wajen warware matsalolin makamashi na nahiyar Turai, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai nuni da ra´ayoyin masana harkokin Afirka. Ta ce ko da yake ƙasashen Afirka musamman na yankin arewacin nahiyar suna da ƙarfin hasken rana da za iya amfani da shi domin samar da makamashi a Turai amma kamata yayi a mayar da hankali wajen ba su fasahar mayar da zafin rana zuwa makamashi maimakon a riƙa romon baka da kuɗaɗen da za su samu idan suka sayarwa nahiyar Turai da wannan ƙarfin hasken ranar.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi