1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin manufofin makamashi a ƙasar Japan

March 10, 2012

Shekara guda kenan cif da aukuwar haɗarin nukiliya a tashar Fukushima a ƙasar Japan, domin kiyaye gaba gwamnati ta tsara sabbin manufofi game da makamashin.

https://p.dw.com/p/14IqD
TOKYO, Japan - Photo taken from a Kyodo News helicopter on Dec. 15, 2011, shows the Fukushima Daiichi nuclear power plant in Fukushima Prefecture, northeastern Japan. Prime Minister Yoshihiko Noda said Dec. 16 the plant has achieved a stable state of cold shutdown, nine months after the outbreak of one of the world's worst nuclear accidents. (Kyodo)
Tashar nukiliyar FukushimaHoto: picture alliance/Kyodo

A matakin wucin gadi yanzu haka a ƙasar Japan an rufe kusan ɗaukacin tukwane 54 dake sarrafa makamashin nukiliyar. Sai dai abin jira a gani shine yiwuwar rufe tashar ɗungurungum.

Firaministan Japan Naoto Kan na ɗaya daga cikin 'yan siyasa ƙalilan waɗanda suka baiyana muradin kawo sauyi ga harkar makamashi. A lokacin mulkinsa ne ya ƙaddamar da wani yunƙuri na tsara sabon shirin makamashi ga ƙasar Japan.

" Shirin da ake da shi a yanzu shine samar da kashi 50 cikin ɗari na makashin ta hanyar nukiliya yayin da za'a samar da kashi 20 cikin ɗari kuma daga sabbin dabarun makamashi. A saboda haka wajibi ne mu sake nazarin waɗannan manufofi da kyau domin samar da sabon tsari mai ɗorewa".

FILE - In this April 12, 2011 file photo, Japanese Prime Minister Naoto Kan reacts during a press conference in Tokyo, one month and one day after the massive earthquake and tsunami devastated northeastern Japan on March 11. Japanese Prime Minister Naoto Kan said Friday, Aug. 26, 2011, he is resigning after almost 15 months in office.(Foto:Koji Sasahara, File/AP/dapd)
Tsohon Firaminista Naoto KanHoto: dapd

Sabuwar manufa kan makamashi

Jim kaɗan kafin ya yi murabus Naoto Kan ya gabatar da daftarin samar da sabbin dabarun makamashin ga majalisar dokoki sai dai kuma dokoki masu nasaba da wannan, da suka shafi alal misali tsarin kuɗin wuta har yanzu ba'a samar da su ba. Ana fatan kammala shirin sabuwar manufar makamashin a tsakiyar wannan shekarar. Akiko Yoshida ta yi tsokaci tana mai cewa " Akwai zaɓin manufofi guda uku waɗanda za'a iya ɗaukar kowanne daga ciki. Na farko dai shine rufe tashar makamashin nukiliyar ɗungurungum, ko da yake wannan ba zaɓi ne da mahukunta za su yi hanzarin ɗauka ba idan akwai wasu damammaki musamman na janyewa daga makamashin nukiliyar sannu a hankali. Ko ma dai wace shawarar aka ɗauka matsalar ita ce shin yaushe ne za'a aiwatar da matakan cikin hanzari ".

Ba za'a gina sabuwar tashar nukiliya ba

Mai riƙon kujerar Firaministan na yanzu Yoshihiko Noda ya baiyana ƙarara cewa ƙasar ba za ta sake gina wata sabuwar tashar nukiliya ba, sai dai yana ganin wajibi ne a sake tsarin aikin tashoshin da ake da su a yanzu. Amma kuma kafin a yi hakan wajibi ne sai an sami amincewar al'umomin da abin ya shafa musamman mazauna yankin da tashar nukiliyar ta ke. Sai dai kuma wasu na nuna adawa.

ARCHIV: Evakuierte Bewohner aus Futaba, einem Ort in der Naehe des durch den Tsunami zerstoerten Kernkraftwerkes Daiichi, Praefektur Fukushima, kommen in ihrer neuen Notunterkunft in der Saitama Super Arena in Saitama, in der Naehe von Tokio an (Foto vom 19.03.11). Bildpaket zum Fukushima-Jahresrueckblick "Im Jahr des Super-GAU". (zu dapd-Text) Foto: Eugene Hoshiko/AP/dapd
Hoto: dapd

" Wannan matashin cewa yake ba zan bada goyon baya a sake buɗe tashar ba matuƙar ba za'a iya tabbatar da kariyar lafiyarmu ba". Shima dai wannan yana baiyana ra'ayinsa ne yana cewa idan aka aka rufe tashar makamashin nukiliyar da ta ke aiki, hakan zai shafi yanayin tattalin arziki da kuma rayuwar al'umma. Tsawon lokaci muna zaune har ma mun saba rayuwa da tashar nukiliyar, muhimmin abu dai shine wajibi ne a tabbatar da kariya da tsaro.

Inganta matakan kariya a tashar nukiliya

Mafi akasarin jama'a dai sun yi amannar cewa ba za su iya rabuwa da makamashin nukiliyar ba. Babu dai rawar da tsohon Firaminista Naoto Kan zai iya taka a nan. Akwai dai damuwa game da ƙarancin wutar lantarki a Japan inda cikin hanzari aka sake bude tsoffin tashoshin lantarkin masu amfani da mai. Farashin man fetur da gas na iya ƙaruwa wanda kuma ka iya sanya kuɗin wutar lantarkin shima ya ƙaru.

Domin samun biyan buƙatar wutar lantarkin musammam a lokaci na sanyin hunturu, an shawarci japanawa su yi ƙoƙarin tattalin wutar lantarkin. A kwanannan hukumar samar da wutar lantarkin ta fidda sabbin alƙaluma wanda ya nuna ƙarin kuɗi kaɗan na farashin wutar lantarkin idan aka kwatanta da abin da ake biya kafin haɗarin tashar nukiliyar ta Fukushima.

Mawallafa: Peter Kujath/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani