1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu 'yan ta'adda sun kai hari a wani Otel a Somaliya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 10, 2015

A kalla fararen hula shida ne suka rasa rayukansu a yayin wani harin ta'addanci da mayakan kungiyar al Shabaab suka kai a Otel din Wehliya da ke tsakiyar babban birnin kasar Mogadishu.

https://p.dw.com/p/1FwxV
Harin ta'addanci a Somaliya
Harin ta'addanci a SomaliyaHoto: M. Abdiwahab/AFP/Getty Images

Wani jami'in dan sanda mai suna Umar Ali ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters faruwar lamarin inda ya kara da cewa tun da farko wani dan kunar bakin wake cikin wata mota makare da bama-bamai ne ya doki kofar shiga Otel din nan take kuma ya tayar da bam din tare da hallaka kansa, kafin daga bisani wasu kuma dauke da bindigogi su mamaye Otel din. A nasa bangaren wani jami'in tsaron gwamnatin kasar ta Somaliya Mohamed Guhad da ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa an hallaka 'yan ta'addan uku baya ga gudan da ya tashi bam din da ke makare cikin motar. A wani labarin kuma 'yan ta'addan sun sake kai hari a wani Otel din na daban da ke kusa da fadar gwamnatin kasar.