Sabon kundin tsarin mulki a Somaliya
August 2, 2012Talla
Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya taya ƙasar Somaliya murnar samun sabon kundin tsarin mulki. Wannan ya zo sa'o'i kaɗan bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar da wakilan ƙabilu 800 su ka yi. Bisa sabon tsarin mulkin mata suna da ta ce wa, ciki harda iya zubar da ciki idan rayuwar mace ta shiga haɗari.
Ƙasar ta Somaliya ta shafe fiye da shekaru 20 bata da cikakkiyar gwamnatin tsakiya. Kazila wa'adin dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD zai kawo ƙarshe cikin watan Agusta, yayin da ake saran a wannan lokaci, ƙasar za ta samu sabuwar majalisar dokoki da sabon Shugaban ƙasa.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman