1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a Somaliya da yaki ya daidaita

Mohammad AwalJuly 18, 2013

Tashe-tashen hankula a yankin Jubaland mai 'yancin cin gashin kai dake kudancin Somaliya na barazana ga karfin ikon gwamnatin tsakiya a birnin Mogadishu.

https://p.dw.com/p/196pX
FILE - In this Wednesday, Dec. 14, 2011 file photo, Kenyan army soldiers sit on a currently unused fishing boat on the white sand shore of the seaside town of Bur Garbo, Somalia. Kenya's military said Friday, Sept. 28, 2012 that its troops attacked Kismayo, the last remaining port city held by al-Qaida-linked al-Shabab insurgents in Somalia, during an overnight attack involving a beach landing. (AP Photo/Ben Curtis, File)
Hoto: dapd

Bari mu fara da jaridar die Tageszeitung wadda ta mayar da hankali a kan rikicin dake ci gaba da daidaita kasar Somaliya.

"Masu adawa da gwamnatin tsakiyar Somaliya sun samu galaba a gwagwarmayar rike madafun iko a kewayen tashar jiragen ruwa ta Kismayo. Bayan mummunan fada da ya janyo asarar rayukan mutane da yawa, Sheikh Ahmed Madobe ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban yankin Jubaland mai ikon cin gashin kansa dake kudancin kasar ta Somaliya da yaki ya daidaita. Shi ne kuma ke iko da birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa. A karshen mako ya kai ziyara Puntland wani yanki da shi ma ke da 'yancin cin gashin kai dake arewa maso gabacin kasar. Ita dai gwamnatin tsakiya a Mogadishu dake samun goyon bayan kasa da kasa ta ce an yi mata makarkashiya inda ta zargi dakarun Kenya da aka girke a kudancin kasar da fakewa da yakin da suke yi da masu kishin addini, suna goyon bayan yunkurin kafa wata kasa a yankin na Jubaland. Rikicin na Jubaland dai na da fuskoki guda uku. Da farko rikicin na da nasaba da gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin kabilun yankin wanda zai ba su iko da tashar jiragen ruwan Kismayo mai muhimmanci wajen fataucin gawayi zuwa kasashen yankin tekun Gulf. Rikicin na da kuma alaka da raba madafun iko tsakanin gwamnatin tsakiya da yankunan kasar. Sabon shugaban kasa Hassan Sheikh Ahmed bai amince da shugabannin Jubaland dake adawa da juna ba, abin da ya harzuka yankin Puntland mai ikon cin gashin kai, suna zargin shugaban na Somaliya da rashin mutunta kundin tsarin mulkin kasa. Rikicin ya kuma shafi kasa da kasa, domin makwabciyar Somaliya wato Kenya na da burin ganin an kafa wata gwamnati mai dasawa da ita a Jubaland. Wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce dakarun Kenya na samun nasu kaso a hada-hadar da ake yi a tashar jiragen ruwan Kismayo."

Kisan gilla a wata makaranta dake Yobe

An rufe makarantu bayan kisan gilla, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung inda ta labarto cewa hukumomi a Najeriya sun zargi kungiyar Islama da hannu a wannan aika-aika.

Pupils of preliminary school in Abuja, Nigeria. (10.03.2009). Foto: LEHTIKUVA / Antti Aimo-Koivisto +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

"Gwamnan jihar Yobe ya ba da umarnin rufe makarantu har zuwa sabuwar shekarar karatu dake farawa a watan Satumba biyo bayan kisan gillan da aka yi wa wasu ‚yan makaranta 21 da malami daya a kauyen Mamudo dake jihar. Rahotannin farko sun ce mutane 42 aka kashe. Har in ya tabbata cewa kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram ta aikata wannan ta'asa to hakan na zama babban koma-baya ko ma abin kunya ga sojojin Najeriya wadanda tun a tsakiyar watan Mayu suka karfafa matakan tsaro da farmakin da a jihohin nan uku na arewa maso gabacin Najeriya, wato Borno da Yobe da kuma Adamawa dake zama tungar masu kishin addini. Sojojin dai na ikirarin murkushe kungiyar ta Boko Haram wadda babu cikakken bayani game da karfinta. Sai dai kisan gillan na kauyen Mamudo ya tabbatar da akasin wannan ikirari."

Kungiyar M23 na fuskantar hare-hare

Some Congolese rebellion's soldiers arrive at their headquarter in Goma, 12 August. Laurent-Desire Kabila, the embattled president of the DRC, was holding a cabinet meeting in the country's second city, Lubumbashi today as rebels were advancing on Kinshasa, having captured much of the east of the country and several key towns in the southwest. dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanzu kuma sai garin Goma na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo inda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito cewa: "a daidai lokacin da dakarun gwamnati da 'yan tawayen kungiyar M23 suka ja daga a kewayen garin na Goma dake gabacin Kongo, kungiyoyin matasa ne dauke da adduna da masu ke kai wa 'ya'yan kungiyar M23 hare-haren wadanda su kuma ba su yi wata-wata ba suka mayar da martani. Yanzu haka dai kungiyar ta M23 dake zama kungiyar 'yan tawaye mafi girma a gabacin Kongo wadda kuma a bara warhaka ta karbi iko da ilahirin yankin kan iyaka tsakanin Uganda da Ruwanda, tana fuskantar hare-hare daga kowane bangare. Kungiyar dai na zargin rundunar sojin Kongo da mara wa matasa 'yan banga baya."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu