sabulun yaki da zazzabin cizon sauro
March 22, 2017Mafi akasari da al-muru sauro yake fara farautar jama'a, wadda kuma shi ke haddasa zazzabin Malaria, cutar da ke kashe mutane kusan miliyan guda a kowace shekara. Gerard Niyandiko wani matashi ne mai ilimin hada sinadarai, kuma a yanzu haka ya kirkiro da wata sabuwar hanyar yakar cutar da kuma sauron dungurungum. Manufar da yake so ya cimma kuma ita ce ceto rayukan masu fama da cutar kimanin 100,000, nan da shekarar 2020.
Sai dai kuma ba abu ne mai sauki ba, saboda a kowace shekara a kan kashe makudan kudade da suka kai dala miliyan dubu 2, wajan yakar cutar, amma kuma duk da haka zuwa yanzu yunkurin sun gaza kaiwa ga cimma nasarar fatattakar cutar.
Gerard ya ce yawancin hanyoyin da ake tunkarar lamarin akwai matukar tsada sannan kuma ba'a gwada su yadda ya kamata. Gerard ya kara da cewa yana so ya gwada wani abu daban, mai sauki amma kuma wadda zai yi tasiri sosai.
Sabulun da Gerard yake magana a kai, ana kiran shi ne da suna Faso, ba kuma wanki kadai ake yi da shi ba, hatta kamshin sa ma yana kashe sauro. abubuwan da aka hada sabulun dai yawanci daga ya'yan itatuwa na gida ne. Da daddare, gidan sauro mai dauke da magani, ya kan nisanta mutum da sauro, amma kuma da rana zuwa maraice lokacin da sauron yafi fitina, kariya kalilan mutum yake da ita. Wannan tunani na hada sabulun dai ya zo wa Gerard ne a lokacin da yake karatun digirin sa na biyu ne a jami'ar birnin Wagadugu fadar gwamnatin kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka.