1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar zanga-zanga a birnin Ouagadougou

February 7, 2015

A wani mataki na kama hanyar sanya kafar wondo guda da dakarun da ke tsaron fadar tsofon shugaban ƙasar ta Burkina Faso, ƙungiyoyin fararan hulla sun yi kiran wani babban taron gangami.

https://p.dw.com/p/1EXeR
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Dubban mutane ne suka fito a yau ɗin nan a birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso, inda suke neman da a rushe dakarun da ke tsaron fadar tsofon shugaban ƙasar Blaise Compaore, batun da ya haifar da babban cece kuce a wannan makon a ƙasar ta Burkina Faso, inda ta kai har dakarun na fadar tsofon shugaban ƙasar suka nemi da Firaminista Isaac Yacouba Zida da ya fito daga cikinsu da ya yi murabus.

Ƙungiyoyin fararan hulla ne dai suka kira wannan taron gangamin don nuna ƙin amincewarsu da take-taken na sojojin da ke tsaron fadar tsofon shugaban ƙasar, inda masu zanga-zangar suka yi ta rera cewar, suna buƙatar da a rushe wannan runduna,

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane