1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakaon zaɓen dattijai a Japan

July 11, 2010

Gwamnatin japan ta sha kayi a zaɓen 'yan majalisan dattijai da ya gudana a ƙasar a wannan lahadin.

https://p.dw.com/p/OGM6
Firaminista Naoto Kan na JapanHoto: AP

Gwamantin Japan ta yi asarar rinjayen da ta ke da shi a majalisar dattijan ƙasar, biyowa bayan kayin da jam'iyar da ke kan karagar mulkin ta sha a zaɓen da ya gudana a yau. ƙididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar jim kaɗan da rufe runfunan zaɓe ta nunar da cewa, kujeru 44 jam'iyar PDJ ta firaminista Naoto kan ta lashe, yayin da ɓangaren adawa ya tashi da kujeru 51. Aƙalla Kujeru 56 jam'iyun da ke cikin gwamantin ƙawance ke bukata kafin samun nasara.

Sai dai wannan shan kayin ba zai sa a tsige firimiya kan daga muƙaminsa ba, domin jam'iyarasa ce ke da hurunmin naɗa rabin membobin majalisar ta dattijai da ta ƙunshi kujeru 242. Amma zai bukacin ƙulla ƙawance da wasu ƙarin jam'iyu domin samun damar aiwatar da mahimman sauye-sauye da ya ke bukata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal