SiyasaJamus
Matakin gaba kan rigakafin corona na AstraZeneca
April 7, 2021Talla
A rahoton karshe kan binciken, daraktar hukumar Emer Cooke ta shawarci jama'a kan ci gaba da amfani da rigakafin don yakar annobar ta COVID-19.
Bisa kwararan hujojjin bincike na kimiyya, ta ce allurar na da matukar amfani kana ta na ceto rayuka da dama, kazalika hukumar ba ta sanya wasu dokoki kan allurar ba koma kayyade shekarun wadanda za a yi wa.
Zurzurfan binciken hukumar dai na zuwa ne baya da kasashen Turai da dama suka dakatar da amfani da allurar rigakafin corona na kamfanin AstraZeneca a watan da ya gabata bisa zargin haifar da daskarewar jini ga wadanda aka yi wa.