240212 Somalia-Konferenz Abschluss
February 24, 2012An kammala taron kasa da kasa akan batun halin da kasar Somaliya ke ciki.Ranar Alhamis aka buda taron a birnin Landan na Ingila wanda ya hada sama da kasashe 50 da Majalissar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma kungiyar hadin kan Larabawa inda suka share wuni daya suna tattaunawa akan makomar kasar ta Somaliya da ta kwashe fiye da shekaru 20 tana fama da fadace-fadace.
Kasar ta Somaliya ta fada ne cikin wani mawuyacin hali tun bayan faduwar gwamnatin shugaba Siad Bare a shekara ta 1991.
Kasashen duniya sun dai jima suna yunkurin maido da doka da oda a kasar al'amarin na cutura. A shekara 1993,Amurka ta aika da sojojinta da nufin fatatakar kungiyoyin tawayen, a lokacin mulkin Bill Clinton,to saidai basu samu shawo kan lamarin ba.
Yanzu haka dakarun Kungiyar Gamayyar Afrika ne ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a kasar.
Taron na Landan ya dubba irin matsalolin da ke tauye zaman lafiya da kuma irin ci-gaban da aka samu a kasar a yakin da tarayyar Turai kewa jagoranci da 'yan fashin ruwan tekun gabar kasar da ake dangantawa da kungiyar Al-Shabab ta 'yan tsautsauran kishin islama.
Taron Landan ya cimma nasara?
A lokacin da yake jawabin buda taron, Firamiyan Birtaniya David Cameron,ya bayana haduwar a matsayin wata kafa da zata basu damar kubutar da kasar da ke cikin kunci.
A nasu bangaren shugaban kasar ta Somaliya Cheik Sharif Ahmed da Firamiyansa Abdiweli Mohamed Ali,sun nuna matukar goyan bayansu ga wannan taron inda shugaban kasar ya ce babban mahimmin abunda ya fi daukar hankalin kowane dan kasar somaliya shine samar da dawamaman zaman lafiya.
A cikin wani jawabin da ta yi Sakateriyar Harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta ce an dai jima ana tafka ruwa kasa tana shanyewa,lokaci ya yi na duniya ta maida hankali ga ceto Somaliya. inda ta bayyana karin miliyan 68 na dallar Amurka a matsayin gudunmuwar Amurka a yankin kafon Afrika baki daya.
To saidai duk da kyaukyawan niyar da kasashen ke dauka ana ganin akwai sauran rina a kaba muddun ba a magance matsallar tsaro ba inda masu kishin islaman kungiyar Al-Shabab suka kulla dangantaka da Al-Qa'ida a farkon watan nan.Tuni kuma masu nazarin al'ammuran kasar ke ganin wannan taron an yi shi ne ba dan dai ya bullar da wani maganin lamarin ba inji Gerard Prunier kwarare akan yankin kafon Afrika:Ba mai bukatar zuba kudinsa cikin Somaliya,Kamar kullum za a basu wasu 'yan kudaden da basu taka kara suka karya ba wadanda kuma za a biyar sahunsu a sace. Duniya na fama da rikicin tattalin arziki,ga matsalar yankin Gabas ta Tsakiya, ga matsaloli barkatai kama daga Pakistan zuwa Isra'ila wa zai tunawa da su? Ai wadannan abubuwan,sune za su fi daukar hankalin Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Turai amma ba wai Somaliya ba.
Har yanzu da sauran rina kaba wajen tabbatarada tsaro a Somaliya
Babban Sakataran Majalissar Dinkin Duniya Ban-Ki Moon,ya bayyana cewar wannan taron shine hanyar da zata kawo canji a kasar ta Somaliya,inda ya kara da cewar Majalisar zata iya nata kokari gurin bada hadin kai ga duk wata bukata ta maido da doka tare da shimfuda demokradiya a kasar.
To saidai a cewar Gerard Prunier,wannan ba shine karo na farko ba da ake wannan yunkurin: Ina da shakku matuka akan batun kamar dai yadda aka sha bayanawa ne a ciikin sauran taruruka 14 na baya a kan kasar. Ana ganin wannan killa shine na kwarai,gaskiya babu tabbaci. A ma dauka an kawarda 'yan kungiyar Al-Shab daukacin yankin kudancin kasar,ba zai hana 'yan fashin ruwa ci-gaba da ayukansu ba.Wannan kuma ba wani abu bane illa kawai rashin kimtsi ne da hadin kai,babu wani cikkaken sa ido akai,bai dace ba.
Yanzu haka dai an zuba ido ne ga dakarun kasa da kasa na kungiyar Afrika ta AU da ke aikin wanzarda zaman lafiya a kasar wadanda ake bukatar adadinsu ya kai a kalla 17.731.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita:Yahouza Sadissou Madobi