sakamakon zaɓen yan majalisun wakilai a Japan
July 30, 2007Talla
Duk da mummunan kayin da jam´iyar sa, ta sha a zaɓen yan majalisun wakilai da ya wakana jiya a ƙasar Japon, Praminista Shinzo Abe, ya ce allabaram ba zai murabus daga muƙamin sa ba.
Sakamakon zaɓen, da aka bayyana yau a hukunce, ya tabbatar da cewar jam´iyar PLD ta Praminista da abikiyar ƙawancen ta, sun samu kujeru 46 kaccal, daga jimmilar yan majalisun wakilai 121 da a ka zaɓa.
Tun girka wannan jam´iya, a shekara ta 1955 wannan shine karo na farko, ta ba ta samu rinjaye ba, a Majalisa.
Sakamakon ya ba jam´iyar adawa ta PDJ gagaramar nasara.
Masu lura da harakokin siyasa a ƙasar Japon, na hasashen cewar, ya zama wajibi ga Shinzo Abe ya yi murabus, domin abun na da matuƙar wahala ya gudanar da mulki ba tare da rinjaye ba a Majalisa.