1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sama da masu zanga-zanga 50,000 ke taro a Cologne

Yusuf Bala Nayaya
April 22, 2017

Kimanin 'yan sanda 4,000 ne dai aka jibge a wannan birni domin kaucewa taho mu gama da ake tsammani tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta AfD da masu adawa.

https://p.dw.com/p/2biZY
Köln vor dem  AfD-Parteitag
Hoto: picture alliance/dpa/O.Berg

Sama da masu zanga-zanga 50,000 ne ake tsammanin su bayyana a birnin Cologne na nan Jamus a wannan rana ta Asabar inda masu adawa da manufofin jam'iyya mai kyamar baki AfD, za su yi gaba-da gaba da magoya bayan jam'iyyar da ke shirin taro mafi girma ga jam'iyyar a tarihinta na shekaru hudu.Kimanin 'yan sanda 4,000 ne dai aka jibge a wannan birni domin kaucewa taho mu gama da ake tsammani tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta AfD mai buri na Turai sai 'ya'yan Turai da masu adawa da wannan manufa ta jam'iyyar.Hannelore Kraft, firemiyar jihar North-Rhine Westphalia, jihar da za a yi taron a cikinta da jagoran jam'iyyar Green Cem Ozdemir ana sa ran za su yi jawabi a taron da zai adawa da manufofin na AfD a wannan rana ta Asabar.Taron na kwanaki biyu dai na zuwa ne bayan da jagorar ta jam'iyyar kin jinin bakin  Frauke Petry ta bada sanarwar cewa ba ta niyya ta jan ragamar jam'iyyar a zaben da za a yi na gama gari a watan Satimba a nan Jamus.