Sakon saki mata ta salula a Saudiyya
January 8, 2019Talla
Daga ranar Lahadin da ta gabata, kotunan kasar za su bukaci mazan aure su aika wa matansu shaidar saki ta hanyar sakon wayar salula, ba tare da sanarwa alwaliyen matan ba, kamar yadda ake yi a da, batun da wasu ke yi wa kallon ci gaba ne na irin 'yanci da sakin mara ga matan kasar ta Saudiya da yarima mai jiran gadon kasar Muhammad Bin Salman ya faro. Mahukuntan na Saudiyya dai sun sha nuna cewar matan kasar sun jima suna shigar da kara a kotunan kasar kan mazajensu da ke sakinsu ba tare da saninsu ba.