1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhuna kan zaben shugaban Burkina Faso

Mouhamadou Awal BalarabeDecember 4, 2015

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan lashe zaben shugaban kasar Burkina Faso da Roch Marc Christian Kabore ya yi da kuma kafa sansani Soji da China ta yi a Jibuti.

https://p.dw.com/p/1HHME
Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Roch Marc Christian Kabore
Hoto: DW/K. Gänsler

Cikin sharhin da ta yi, Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce Kabore ne zakaran da Allah ya nufa ta cara a zaben shugaban Burkina Faso, bayan shafe watanni da al'ummar suka yi na gagwarmayar dora kasar ta yammacin Afirka kan tafarkin demokaradiya. Sai dai kuma Jaridar ta ce kasancewar Kabore ya taba zama dan gaban goshin tsohon shugaba Blaise Compaore, wannan tabon zai iya zame masa kadangaren bakin tulu. A cewarta dai ya zama wajibi a gareshi ya dauki matakan inganta halin rayuwar 'yan Burkina Faso, ko kuma su sake fantsama kan tituna domin su nuna masa gajiyawarsa.

Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Wähler
'Yan Burkina faso na son Kabore ya inganta rayuwarsuHoto: DW/K. Gänsler

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland cikin sharhinta cewa ta yi zababben shugaban Burkina faso Roch Kabore na da jan aiki a gabansa. A cewarta dai dole ne ya wadata duk 'yan Burkina faso da ruwa mai tsabta kamar yadda kundin tsarin mulki kasar ya tanada. Sannan kuma akwai bukatar inganta tsarin kiwo lafiya da na ilimi, saboda kashi biyu bisa uku na 'yan kasar da ke da kasa da shekaru 15 da haihuwa ba su iya karatu da rubuta ba. Ga shi kuma Burkina Faso na fama da dimbim 'yan zaman kashe wando

Wani batu da ya dauki hankali jaridun Jamus a wannan makon shi ne kafa sansanin soji da China ta yi a karon farko a wata kasa ta Afirka wacce ba wata ba ce illa Jibouti.

Simbabwe Harare Besuch Xi Jinping
Shugaba Xi Jinping na neman anginzo tsaro a AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/A. Ufumeli

Jaridar Berliner Zeitung ta ce a wannan Alhamis, shugaban China Xi Jinping da takwarorinsu na kasashen Afirka sun fara taron kolinsu a Afirka ta Kudu da nufin nazarin kyakyawar dangantakar da ke tsakaninsu. Sai dai kuma wannan ya zo ne lokaci kadan bayan da China ta yi nasarar cimma yarjejeniya da gwamnati Jibuti, da ta bata damar kafa sansaninta na soji, wacce ke zama ta farko a wajen kwaryar kasar ta China.

Jaridar ta ce a hukumance dai, China ta dauki wannan mataki ne don kare mashigin ruwanta da ma teku Aden daga hare-haren 'yan fashi. Amma kuma a zahiri fadar mulki ta Beijing na neman yada angizonta a fannin tsaro a nahiyar Afirka, shigen wanda Amirka da Faransa ke yi.

Jaridun na Jamus ba su bar batun tsaro da ke addabar wasu kasashen Afirka a baya ba. New Germany ta yi dogon sharhi a kan wannan batu, inda ta ce kasashen Afirka da dama na fuskantar kalubalen ta'addanci, lamarin da ke dakile duk fatan da suke da shi na samun ci gaba a fannin tattalin arziki.

Nigeria Boko Haram Terrorist
Boko Haram ta sa Najeriya da Nijar da kamaru da Chadi a gabaHoto: picture alliance/AP Photo

Jaridar ta ce kusan a duk rana ta Allah, tsiraru da ke tayar da fitina da sunan Islama na kai hare-hare a kasashen Najeriya da kamaru da Niger da Mali da Somaliya da Kenya domin rarraba kawunan mutane kan manufar da suka sa a gaba. Jaridar ta kara da cewa Kungiyoyin Boko Haram da al-Shabaab da Is da sauransu, ba wai kiristoci kawai suke kashewa ba, har da Musulmin wadannan kasashe ma na cikin halin ni 'yasu. Su na bin kasuwanni da duk cibiyoyin neman kudi wajen tarwatsa bama-bamai da suke daurawa. Ta ce ya wajaba kasashen duniya su taimaka wa Afirka murkushe 'yan ta'adda, domin idan ba haka za su yadu tamkar farin dango i zuwa wasu kasashen wannan nahiyar.

Papst Franziskus besucht die Zentralmoschee in Bangui
Paparoma Francis ya nemu Musulmi da Kiristan Bangui su hada kaiHoto: Reuters/S. Rellandini

Bari mu karkare da ziyarar da shugaban darikar Roman katolika Paparoma Francis ya kai wasu kasashen Afirka guda uku. Jaridar Dir Tageszeitung ta ce a zangonsa na karshe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Paparoma ya shiga cikin babban masallancin birnin Bangui don nunawa cewar kirista da Musulmi duk Allah suke baitawa, saboda haka 'yan uwan juna ne.