Shekaru 50 na baje kolin fina-finan Afirka FESPACO
A watan Fabrairun 1969 aka fara bikin baje kolin fina-finan Afirka a Burkina Faso. A yanzu an fara karo na 26. Bikin da aka gama a Berlin wato Biennale bangare ne mai matukar muhimmanci. Waiwaye.
Bikin baje kolin fina-finan Afirka
Guda daga cikin mafi dadewar bikin baje kolin fina-finai kuma mafi muhimmanci a nahiyar Afirka na cika shekaru 50: Bikin baje kolin fina-finan Afirka da na talabijin a birnin Ouagadougou wato FESPACO -an fara shi ne a watan Fabrairun 1969.
Tasirin Sinima
Kamar kowanne lokaci, shima bikin baje kolin fina-finan karo na 26 da aka fara a ranar 23 ga wannan wata na Fabrairu a Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, an fara ne da bushe-bushe. Sukuwar dawaki na zaman jigo na bikin. Babbar kyauta a wannan rana ita ce ta "Etalon d'Or de Yennenga"-zinare ne da aka sanya masa sunan gwarzuwar 'yar sarki gimbiya Yennenga.
Ouagadougou: Babban birnin Sinima
Akwai ma'abota zuwa Sinima, ciki har da ministar al'adu, wadda ta assasa bikin kasar Obervolta a wancan lokaci. Kawo yanzu an nuna fina-finai 2140 kuma 160 sun lashe kyaututtuka. Tarihi ya nunar da cewa fim din "Place des Cinéastes" da aka nuna tun a shekara ta 1987 ne ya tabbatar da birnin na Ouagadougous a matsayin babban birnin Sinima.
Ousmane Sembène da mafarkin samun karbuwa
Ci-gaban Sinima a Afirka ya karfafa ne da tallafin Turawan mulkin mallaka. A kasashen Afirka ta Yamma rainon Faransa, Ousmane Sembène na daga cikin mutane na farko da suka fara bayar da umurni a fim. A cewar Sembène marubuci na farko, fina-finai wata kafa ce ta isar da sako ga al'umma baki daya. Sai dai yaduwar fina-finan Afirka na ci gaba da zama matsatalar da ba ta shafi baje kolinsu ba.
Gwagwarmayar bayyana ra'ayi
Da fari, Sinimar ta Afirka na da manufa ta siyasa: Kullum ana magana kan yadda za a kawo karshen mamayar al'adun Turawan mulkin mallaka da kuma yakar zamansu a kasashen da ke karkashinsu. Fim din "Med Hondos" na Sarraounia ya bayyana tarihin wani jagora da ya yaki mulkin mallakar Faransa. Fim din ya lashe babbar kyautar zinare ta baje kolin fina-finan Afirkan wato "Etalon d'Or" a shekara ta 1987.
Dokin kudancin Saharar Kalahari
Masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai a Afirka, sun yi nasarar mayar da hankali kan tarihi. Fim din "Drum" Zola Maseko ya nuna rayuwar 'yan jarida a garin Sophiatown karkashin gwamnatin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. A shekara ta 2005 fim din ya lashe kyautar na daya a Afirka ta Kudu, na biyu a kasashen da Birtaniya ta mulka. Abin naci gaba: Najeriya da Habasha za su karbi kyauta ta gaba.
Fita daga kangi
Wasu na kokarin kwatar 'yancinsu a bikin baje kolin: Sai a shekara ta 2010 ne mata suka fara shiga dumu-dumu cikin harkar fina-finai har ma suke shirya nasu bikin baje kolin duk shekara har ma a FESPACO. Naky Sy Savané ta fito a fim din "Frontières" da ya nuna yadda wata mata 'yar kasar Côte d'Ivoire ke safarar kaya ta haramtacciyar hanya domin tallafawa karatun 'ya'yanta.
Tsallake kan iyakokin nahiyar
Akwai tababa kan yanayin dangantaka da sauran kasashen duniya. A shekara ta 1987 masu fina-finai daga Afirka suka fara samun damar halartar bikin baje kolin. Sai a shekara ta 2015 ne suka fara fatan lashe babbar kyauta. 'Yan Afirka kalilan duniya ta san da zamansu. Abdrahmane Sissako ne dan Afirka na farko da ya lashe kyautar fim ta "César" ta Faransa, da fim dinsa na "Timbuktu" a shekara ta 2015.
Ta'addanci ya kawo cikas
Tsahon lokaci, kasar da ke yankin Sahel na fama da harin ta'addanci. Babban abin firgici, a shekara ta 2016 Otel din Splendid, da ya yi fice wajen sauke manyan bakin da ke halartar bikin baje kolin ya fuskanci harin ta'addanci. Sai dai saboda yadda aka san FESPACO a duniya, harin bai hana a gudanar da bikin da shekara ta zagayo ba. A wannan lokaci tsaro ya inganta.
Amfani da hanyoyi na zamani
Tun a shekara ta 2015 aka fara amfani da hanyoyin zamani a duniya wajen yin fina-finai. Sai dai da fari an dandana kuda kafin komawa tsarin na zamani saboda tsadar da hakan ke da shi. Masu bayar da umurni na biyan makudan kudi ga masu kallo ko kuma gidajen talabijin. Har kawo yanzu masana'antun shirya fina-finan Afirka sun dogara ne ga samun tallafi daga waje.