Shirin fuskantar zabuka a Burkina Faso
May 9, 2015Jam'iyyar ta yi wannan sanarwa ce a wannan Asabar din ya yin wani babban zaman taronta na karko tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Compaore. A farkon watan Afrilu ne dai da ya gabata, majalisar dokokin kasar ta rikon kwarya CNT, ta haramta tsayawa takara ga duk wadanda suka taka rawa, wajan take kundin tsarin mulkin kasar a lokacin da hambararran shugaban kasar ya yi kokarin sake tsayawa takara duk da cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ta Burkina Faso.
Shugaban wannan Tsofuwar jam'iya ta CDP Léonce Koné cikin jawabinsa ya ce, a halin yanzu jam'iyyar tasu zata zagine na ganin ta taka rawar gani a zabukan masu zuwa, inda ya zargi majalisar rikon kwaryar kasar da amincewa da wata doka da ta sabawa demokradiyya.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu