1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Chaina na shirin kulla yarjejeniya

Ramatu Garba Baba
June 22, 2020

Kungiyar tarayyar Turai da Chaina na shirin gudanar da wani taro a wannan Litinin da zummar kulla yarjejeniyar kasuwanci, bayan da suka shafe lokaci suna kai ruwa rana bisa sabanin ra'ayoyi.

https://p.dw.com/p/3e8NZ
Symbolfoto Handelsbeziehungen zwischen China und der EU
Hoto: picture-alliance/dpa/K.Ohlenschläger

Tun bayan sabanin da aka samu a tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da Chaina bayan bullar annobar Coronavirus, a wannan Litinin bangarorin biyu sun amince su gudanar da wani taro don dinke barakar, ganawar da za a yi ta kafar bidiyo, za ta mayar da hankali kan yadda za su sabunta batun bunkasa dama kulla yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu.

A baya shirin ya fuskanci tsaiko bisa zargin Chainan da EU ta yi na sabawa dokokin kasa da kasa, kan matakinta a rikicin yankin Hong Kong da zarginta da yada labaran karya na cewa, gwamnatocin kasashen na EU sun gaza a yakar annobar Coronavirus, gwamnatin Beijing dai, ta musanta wadannan zarge-zargen.

Taron na yau, zai hada da Shugabar hukumar zartaswa ta EU Ursula von der Leyen da Shugaban majalisar Turan Charles Michel da kuma Shugaba Xi Jinping da Firaiminista Li Keqiang.