LMJ
September 9, 2019Talla
A cikin shirin za a ji yadda ta ke kayawa a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin wallon kafa na duniya ta shekara 2022. A wasannin share fagen shiga gasar cin kofin wallon kafa na nahiyar Turai da za a fafata a shekara ta 2020 da ke tafe kuwa, Jamus za ta fafata da kasar Ireland ta Arewa bayan da ta sha kashi a hannun kasar Netherlands da ci hudu da biyu. Muna tafe da karin haske game da gasar cin kofin duniya na kwallon kondo da ake yi a China da ma sauran wasanni.