Cikin shirin za a ji cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya, ya bayar da umurnin maida wata tsohuwar majami'a zuwa masallacin da Musulmi za su fara ibada a cikinsa. Najeriya ta ce jiragen Turai ba za su yi jigila zuwa kasar ba bayan haramta wa 'yan Najeriya shiga kasashensu da Turawan suka yi.