A cikin shirin za aji cewa kakakin majalisar dokokin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya fasa kwai, bayan ikrarin da gwamnatin Najeriya ke yi na cewa sojojinta sun karbe iko da daukacin kananan hukumomin jihar daga Boko Haram. Wasu mahara sun kai farmaki a babban ofishin hukumar zabe ta Inec a birnin Owerri na jihar Imo da ke Najeriya.