A cikin shirin za a ji cewa aNajeriya jami'an tsaro sun bazama neman ‘yan bindigar dajin da suka kai hari a kauyen Kafin–Koro da ke karamar hukumar Paiko ta jihar Niger. A Nijar kuma yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar ta kaddamar ya ritsa da wani alkali da ake zargi da karkatar da wasu kudaden gado.