A cikin shirin za a ji cewa, alkalumma kungiyar agaji ta ICRC sun yi nuni da cewa, kimanin mutane dubu 26 ne suka bace sakamakon rikicin yankin arewa maso gabashin Najeriya. A Nijar, kungiyoyin fararen hula sun yi kira kauracewa kasuwanni sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta.