A cikin shirin za a ji cewa a Jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ta cimma sabuwar yarjejeniya da Jamus kan tallafin kudi domin samar da horo ga jami'an tsaro a kasar. A Najeriya kuwa, likitocin da ke yajin aiki sun ce ko a jikinsu kan ga barazanar ministan kwadagon kasar ya yi na maye gurbinsu da likitocin haya.