A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, sabon Sefeta Janar na 'yan sandan kasar ya yi ikrarin yin aiki ba dare ba rana wajen kakkabe masu aikata miyagun laifuka a kasar. A Nijar kuma, gwamnatin kasar ce ta samu tallafi domin inganta noman tumatir a kasar.