A cikin shirin za a ji cewa, mahajjata sun yi kololuwar aikin hajji na hawan Arfa a kasar Saudiyya, wannan shi ne karon farko da aka samu mahajjata masu yawa a tarihi kuma aka gudanar ba tare da dokokin corona ba. A Nijar, ana kira kan a taimakawa gidajen marayu a lokutan salla domin cire musu da kewar iyayensu.