Shirin ya kunshi martani kan hari da 'yan bindiga suka kai fadar Mai Martaba Sarkin Minna a jihar Neja ta Najeriya da yadda 'yan IPOB masu rajin Biafra a Najeriya suka kafa wata dokar zaman dirshan da kuma batun da ya shafi bai wa kamfanin Faransa damar aikin ma'adinin Uranium a Nijar.