A cikin shirin za ji cewa ana cigaba da zaman zullumi a karamar hukumar Faskari bayan da 'yan bindiga suka sace mata da kananan yara fiye da 30. Batun lafiyar shugabanni a Najeriya na ci gaba da daukar hankalin al'ummar kasar a daidai lokacin da miliyoyin al'umma ke shirin yanke hukunci kan wadanda za su zaba nan da gaba a babban zaben kasar.