Cikin shirin za a ji cewa kasar China na son bunkasa huldar tsaro tsakaninta da nahiyar Afirka. Tuni ta gayyaci shugabannin rundunar sojojin Afirka zuwa Beijing da nufin tattaunawa tare da bullo da sabuwar dangantaka. Taron na birnin Bejing dai an fara shi ne a ranar 26 ga wannan wata na Yuni da muke ciki kuma za a kammala a ranar 10 ga watan gobe na Yuli.