A cikin shirin za a ji cewa, Cibiyar Sasanci tsakanin addinai ta Najeriya na taro da masu ruwa da tsaki don karfafa hanyoyin gujewa rikici ta hanyar fadakarwa a Arewa gabanin zaben 2023. Za kuma a ji yadda dalibai da iyayensu ke cikin damuwa bayan rufe makarantun koyan aikin likita a Gaya na Jamhuriyar Nijar.