A cikin shirin za a ji, yayin da ake biki ranar yaki da cutar shan inna, a Najeriya hukumomi sun ce an nasarar kawar da cutar. A Jamhuriyar Nijar, ma'aikatar magajin garin Damagaram ta gudanar da taron 'yan majalisa. A Ghana masu sana'ar jari bola na amfana da shara tan dubu 12 da ake fitarwa a kullum.