A cikin shirin za a ji cewa ana cikin shekarar karshe ta tawagar sojin Jamus ta Bundeswehr da ke Mali. A Nijar kuwa, wani shahararren mawakin 'Rap' mai suna Ham D Malam, ya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa yara kanana marayu da sauran yara da ke gararamba kan tituna.