A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, Kungiyar kiristocin ta kasar ta yi kira ga limaman Mujami'u da su kiyaye furta kalamai na tunzuri, yayin da ake kara tunkarar babban zaben kasar. A Nijar kuwa, jama'ar Doso za su tarbi sabon sarkin 'yan kokowar gargajiya na jihar wanda ya lashe takobi a gasar ta bana.