A cikin shirin za a ji cewa, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri da zai gwama karatun addini da na zamani a makarantun tsangaya. A Nijar, wata mata ta kai karar wani likita bayan da ya cire wa 'yarta mahaifa ba tare da izinin iyayenta ba. Akwai rahoton Kundin 'yan mata da ya duba matsalar fyade.