A cikin shirin za a ji cewa, shugabannin kungiyoyi na ci gaba da yin Allah wadai da harin da ya hallaka wasu Fulani makiyaya kimanin 40 a jihar Nassarawan Najeriya. A Nijar an bude babba taron kasa karo na farko kan shirya aikin hajji da Umara, domin bitar matsalolin da ke kawo cikas ga tafiyar da aikin hajji a kasar.