A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, gwamnan jihar Jigawa ya sanar da nada Hamim Muhammad Nuhu Sunusi a matsayin sabon sarkin Dutse. A Nijar kuwa, Kwamitin masu bukata ta musamman da suka yi karatu mai zurfi suka kaddamar da wani tsarin na bada horo kan jagoranci da sanin hakkokin masu bukata ta musamman.