A cikin shirin za a ji cewa Hukumar kare hakkin bili'Adama ta Amnesty International, ta bukaci gwamnati mai jiran gado a Najeriya ta tabbatar da cewa kamfanin man Shell ya biya dukannin diyya na yankin Niger Delta. A Nijar, ana nuna damuwa kan matasan da ke zuwa cirani kasar Libiya ke komawa da tabin hankali.