A cikin shirin za a ji cewa a ci gaba da ziyarar da ta ke yi a Najeriya, 'yar fafattukar bunkasa ilimin mata Malala Yousafzai ta gana da kungiyoyin rajin inganta a illimi a Abuja. Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya ta bude sabon wurin bincike domin kula da shige da fiye a kan iyakar Najeriya da kuma Nijar.