A cikin shirin za a ji cewa a Jamhuriyar Nijar, gamayyar kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa na wayar da kan jama'a kan yadda za a yaki matsalar a kowani mataki. A Najeriya kuma, daruruwan 'yan gudun hijira da gwamnatin jihar Borno ta mayar garuruwansu ne ke sake goduwa sakamakon matsalar yunwa.