Shirin ya kunshi yadda iyayen dalibai ke neman gwamnatin Sokoto ta biya kudin tallafin karatu domin rage musu nauyin da suke fama da shi. A Najeriyar ana sukar tsarin rarraba abinci da gwamnatin kasar ta kaddamar da ake cewa ba zai isa ba. A Nijar an kaddamar da yaki da zazzabin cizon sauro da cutar tamowa.