1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Sintiri a Kogunan Somaliya

Zainab MohammedDecember 8, 2008

Ƙungiyar Tarrayyar Turai da shirin tabbatar da tsaro a Ƙahon Afrika ..

https://p.dw.com/p/GBSV
Fashin Jirgin Ruwa a SomaliyaHoto: AP

A yau ne ƙungiyar tarayyar turai Eu take kaddamar da aikin sintirin ruwa na farkon irinsa, daya kunshi Jiragen ruwa shida da jiragen Sama guda uku,waɗanda zasu tabbatar da tsaro a Tekunan dake yankin ƙahon Afrika.

Wannan dai na mai kasancewa gagarumin aikin sintirin ruwa da ƙungiyar ta tarayyar turai ta taɓa kaddamarwa.Kuma jiragen sintirin na fuskantar kalubalen tabbatar da tsaro a tekun yankin da girmansa yakai square km million ɗaya, kogin daya fuskanci fashin jiragen ruwa guda 100 a wannan shekara kaɗai.

Kawo yanzu dai akwai kokwanto dangane da tasirin wannan shin na Turai. Masu nazarin lamuran yau da kullum na ganin cewa, da zai fi dacewa ƙungiyar kasashen turan ta fara tabbatar da zaman lafiya a kasar Somalia,wadda ke fama da rikicin daya ki ci yaki cinyewa, a maimakon farawa da 'yan fashin ruwa.

A ƙarkashin tsarin dai,a shekarar farko jiragen sintiri daga kasashe 8 da suka hadar da Belgium, Britania, Faransa, Jamus ,Girka, Netherlamds, Spain da Sweden, zasu yi rakiya wa jitragen dake dauke da kayayyakin agaji,da samar da kariya daga 'yan fashin jiragen ruwa akarkashin jagorancin Admiral Phillip Jones na Britaniya.

Babban Sakataren ƙungiyar tsaro ta NATO Jaap de Hoop Scheffer yace aika-aikan na daɗa tsananta...

"Lamarin sai kara tsananta yake ,wanda ke zama babbar matsala ga harkokin sufurin jiragen ruwa daga ƙasa zuwa wata ƙasa.Yana da matukar muhimmanci a sa ido a wannan tekun, saboda ya kasance hanya ce da jiragen ruwa sama da dubu 200 ke bi a kowace shekara,kuma a yanzu fasahin jiragen yakai kashi 300 daga cikin 100"

A yanzu haka dai jiragen NATO na tafiyar ta aikin sintirin da ƙarin Jirage a waɗannan koguna.Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier yayi karin haske da hakan a wajen taron NATO a birnin Brussels...

"Mun riga ya munga abunda ya faru a baya,deangane da irin cikas da 'yan ta kifen suka haifar wajen zirga zirgan jiragen ruwa a yankin kahon Afrika"

A cewar babban jami'in kula da harkokin ketare na ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana wannan gagarumin aiki ne daya wajaba akansu...

"Wannan zai kasance aiki ne mai muhimmanci ,wanda keda nufin samar da kariya ta musamman ga ayyukkan tallafi na gaggawa da Majalisar Ɗunkin Duniya ke tafiyarwa tafiyarwa"

Da Headquatar shirin a Northwood dake kusa da birnin London dai, jiragen sintirin zasu fara aiki a kogunan Somaliyan ne, a karkashin jagorancin Admiral Antonios Popaioannou,a yayinda jami'an spaniya da na Holland zasu yi karɓa karɓa bayan wata uku.

Kwararru dai na cigaba da jaddada bukatar maganta matsalar Somalia daga tushe, matsalolin da suka haɗar da talauci da rashin tsaro.