Venezuela na gudanar da zaben sabuwar majalisar wakilai, wanda 'yan adawa suka kaurace masa, kana yawancin kasashen yammaci na Turai ke bayyana shi a matsayin "yaudara" da kokarin shugaba Nicolas Maduro na sake mallake wannan sashi na gwamnati da baya karkashin jam'iyyar da ke mulki.