A cikin shirin za a ji cewar a Najeriya al'ummar jihar Filato na cigaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan sabon hukuncin da kotun daukaka kara dake Abuja ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Joshua, wanda yanzu zai yi shekaru 10 ne a gidan wakafi a maimakon shekaru 14.