A cikin shirin za a ji cewa haramtacciyar kungiyar Biafra ta IPOB ta umarci al'ummar yankin kudancin Najeriya da su yi zaman dirshen a albarkacin ziyarar da aiki da shugaba Muhammadu Buhari ya kai a yankin. A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta kaddamar da wani sabon shirin wadatar da kasar da wutar lantarki