Cikin shirin Najeriya ta samu kwarya-kwaryar nasara kan 'yan ta'adda da sauran masu satar mutane domin neman kudin fansa. A Nijar zaman dirshen aka yi saboda rashin daukar jami'an kwastam da aka ba su horo duk da umurnin da kotu ta bayar da a yi hakan a hukumance.