A cikin shirin za a ji cewa, al'ummar jahohin Katsina da Zamfara musamman mazauna yankunan karkara na cigaba da tsokaci kan matakin sauya wasu daga cikin takardun kudin Najeriya. A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar amincewa da gyaran fuska ga dokar kudaden alawus da albashin yan majalisar.