A cikin shirin za a ji cewa, a Najeriya daliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Nsukka da ke jahar Enugu sun barke da wata zanga zangar nuna kin amincewa da karin kudaden makaranta da hukumar jami'ar ta yi har da kaso dari. A jamhuriyar Nijar, jama'a ne suka shiga damuwa biyo bayan karancin iskan gaz da ake fuskanta.